Luke 2

Haihuwar Yesu

1A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. 2(Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) 3Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

4Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. 5Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. 6Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, 7ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.

Makiyaya da Malaʼiku

8Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare. 9Sai wani malaʼikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai. 10Amma malaʼikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. 12Wannan zai zama alama a gare ku: Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”

13Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da malaʼikan, suna yabon Allah suna cewa,

14“Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,
a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”

15Da malaʼikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”

16Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. 17Saʼad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, 18duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa. 19Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta. 20Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

Miƙa Yesu a Haikali

21A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da malaʼika ya ba shi kafin a yi cikinsa.

22Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji 23(yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”
Fit 13.2, 12
),
24don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa: “kurciyoyi biyu ko ʼyan tattabarai biyu.”
L Fir 12.8


25To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Israʼila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji. 27Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Saʼad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da alʼadar Doka ta bukaci, 28sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa:

29“Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari,
yanzu ka sallami bawanka lafiya.
30Gama idanuna sun ga cetonka,
31wanda ka shirya a gaban dukan mutane,
32haske don bayyanawa ga Alʼummai
da kuma ɗaukaka ga mutanenka Israʼila.”

33Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi. 34Saʼan nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa: “An ƙaddara yaron nan yǎ zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Israʼila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, 35ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”

36Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, 37ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu.
Ko kuwa gwauruwa na shekaru tamanin da huɗu
Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da adduʼa.
38Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

39Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu. 40Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.

Yesu a Haikali

41Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. 42Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga alʼada. 43Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba. 44Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Saʼan nan suka fara nemansa cikin ʼyanʼuwansu da abokansu. 45Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa. 46Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi. 47Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa. 48Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”

49Sai ya ce, “Don me kuke nema na? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?” 50Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.

51Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta. 52Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.

Copyright information for HauSRK